AFCON 2026: Salah Ya Kai Masar Zagayen ‘Yan 16
[ad_1]
Ɗan wasan gaban Liverpool Mohamed Salah ya zura ƙwallo ɗaya tilo a wasan da suka doke Afirika Ta Kudu a yau Juma’a, wannan ƙwallo da Salah ya jefa tayi sanadiyar zuwan ƙasar Masar zuwa zagayen ‘yan 16 na gasar ƙasashen Nahiyar Afirika da aka buga a birnin Agadir, Masar ta zama kasa ta farko da ta kai zagayen 16 a kakar wasan ta bana.
Tauraron na Liverpool Salah, ya jefa bugun daga kai sai mai tsaron raga da Masar ta samu gab da tafiya hutun rabin lokaci.
- Tattalin Arzikin Nijeriya Ya Bunkasa A 2025 — Minista
- “Basirar Kirkire-kirkire A Kasar Sin” Ta Zama Abar Yabo A Duniya A Shekarar 2025
Sai dai kuma alƙalin wasa ya hana Afirka ta Kudu bugun fenariti a ƙarshen wasan lokacin da ta bayyana cewa Yasser Ibrahim ya riƙe ƙwallon da hannu a cikin yadi na 18.
An bai wa ƙasar Masar katin kora a wasan, wanda hakan ya janyo suka dawo mutum 10 kacal a tsakiyar fili, lokacin da aka bai wa wasan baya na dama Mohamed Hany katin gargaɗi sannan aka sake ba shi jan kati, bayan zagaye na biyu a rukunin B, Masar, wacce ta lashe gasar sau bakwai, ta haɗa maki shida wanda hakan ya tabbatar mata da ƙarewa akalla a matsayi na biyu a rukunin.
[ad_2]
Source link