Ding Xuexiang Ya Halarci Bikin Bude Taron Shekara-shekara Na Dandalin Zhongguancun Na Shekarar 2026
[ad_1]
A yau Laraba ne aka bude taron shekara-shekara na dandalin Zhongguancun na shekarar 2026 a birnin Beijing, inda memban hukumar siyasa ta kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta Sin, kuma mataimakin firaministan kasar Ding Xuexiang ya halarci taron tare da gabatar da jawabi.
A cikin jawabinsa, Ding Xuexiang ya bayyana cewa, kasar Sin tana son yin kokari tare da bangarori daban daban, wajen raya tsarin hadin gwiwar kimiyya da fasaha na duniya. Ya kuma bayar da shawarwari guda uku; wato na farko a raya tsarin gudanar da kirkire-kirkire mai bude kofa da hadin gwiwa. Na biyu a bunkasa hadin gwiwar kimiyya da fasaha a fannoni daban daban, don sa kaimi ga nazari daga tushe cikin hadin gwiwa da kuma amfani da sabbin fasahohi, wajen bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasa da kasa. Kana na uku a sa kaimi ga gudanar da harkokin kimiyya da fasaha mai adalci, domin tinkarar hadari, da kalubale a fannonin ka’idoji, da zamantakewar al’umma, da dabi’a, wadanda bunkasuwar kimiyya da fasaha ta kawowa kasashen duniya. (Zainab Zhang)
[ad_2]
Source link