Obasanjo Ya Buƙaci A Kawo Ƙarshen Cin Zarafin Yara Ƙanana
[ad_1]
A ranar Litinin ce Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya yi kira da a ƙara kulawa da yara, yana mai bayyana su a matsayin ginshiƙin makomar kowace al’umma.
Obasanjo ya yi wannan kiran ne yayin da yake karvar baƙuncin shugabannin Ƙungiyar Likitocin Yara ta Nijeriya, ƙarƙashin jagorancin shugabarta, Dakta Ekanem Ekure, a gidansa da ke cikin Olusegun Obasanjo Presidential Library a Abeokuta.
- Rikicin Boko Haram Ya Daɗe Fiye da Yaƙin Basasar Najeriya – Obasanjo
- Gasar Euro 2024: Yadda Kasashe Suka Gayyaci ‘Yan Wasa
Tsohon shugaban ƙasar ya ce likitocin yara na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da lafiyar yara, don haka bai kamata su gaji ba wajen ƙara ɗaga matsayin ƙwarewa da kuma yin ƙoƙari fiye da da wajen kula da yara, waɗanda ya bayyana a matsayin fata da makomar kowace al’umma.
Obasanjo ya ce ko da yake ya daina haihuwa, wasu daga cikin ’ya’yansa ma sun daina haihuwa, amma jikokinsa suna ci gaba da haihuwa, yana mai jaddada muhimmanci da matsayin yara wajen ci gaba da wanzuwar al’umma da zuri’a.
Tsohon shugaban ƙasar ya ce saboda wannan muhimmanci na samun yara masu ƙoshin lafiya a cikin al’umma, zai amince da rawar ba da shawara da ƙungiyar ta ɗora masa, yana mai cewa zai ci gaba da tallafa wa duk wani yunƙuri da ke nufin inganta walwalar yara a faɗin duniya.
Obasanjo ya ce, “A matsayinku na ƙwararru a fannin kula da lafiyar yara, aikinku aiki ne na rai da mutuwa. A matsayinku na likitan yara, kuna da wata ƙwarewa ta musamman domin kuna hulɗa da yara.
“Kuma matsalar kula da yara ita ce ba su kama da manya; dole ne ku iya jin tausayinsu. Idan ni ne manya na zo wurinku, za ku tambaye ni inda nake jin ciwo, ko a dama ko a hagu, yadda nake ji da dare, amma yara ba za su iya faɗin duk waɗannan ba.
“Saboda haka fannin ƙwarewarku na da matuƙar muhimmanci. Don haka aikin da kuka ba ni na zama mai kare haƙƙin yara, zan karve shi da hannu bibbiyu.
“Ba zan ƙara haihuwa ba, domin ’ya’yana sun manyanta, amma ’ya’yana suna haihuwa, jikokina ma suna haihuwa, don haka ba zan tava daina samun yara ba.
“Domin idan na daina, ’ya’yana ba za su daina ba, idan ’ya’yana sun daina, jikokina ba za su daina ba, kuma zagayowar rayuwa tana ci gaba. Saboda haka ina ƙarfafa ku da ku ci gaba da yin iyakar ƙoƙarinku wajen ba da kulawa mafi kyau ga ƴa’yanmu, domin su ne ainihin makomarmu.”
A baya, Ekure ta yaba wa tsohon shugaban ƙasar, tana mai bayyana shi a matsayin fitaccen jigo na duniya da shugaba mai jajircewa wajen inganta walwala da jin daɗin jama’a a faɗin duniya.
Ta ce ƙungiyar ta zo Abeokuta ne domin gudanar da Babban Taron Shekara-shekara na 57 da Taron Kimiyya, kuma tana so tsohon shugaban ƙasar ya zama mai kare walwalar yara.
Ekure ta ce, “Mun zo ne domin roƙonku da ku zama mai kare haƙƙin yaran Nijeriya. Fiye da rabin ’yan Nijeriya yara ne da matasa, kuma su babbar dukiya ce ga ƙasar.
“Abin takaici, waɗannan na fama da cututtukan da za a iya hana su, take haƙƙin bil’adama da walwalarsu, da kuma rashin gina jiki, wanda ke da matuƙar tayar da hankali.
“Shi ya sa muka zo wurinka, domin mun san kana da matsayi na musamman a matsayinka na tsohon shugaban ƙasa dattijo mai daraja, wanda hakan ke sa muryarku ta yi ƙarfi kuma ta yi tasiri.
“Duk abin da kuka faɗa, gwamnati da jama’a za su saurara,” in ji ta.
Da take magana da manema labarai gabanin Babban Taron Shekara-shekara na 57 da Taron Kimiyya na ƙungiyar, Ekure ta bayyana cewa fiye da jarirai 800 na mutuwa a kowace rana, duk da cewa mafi yawancin mutuwar ana iya shawo kanta.
[ad_2]
Source link