’Yan bindiga sun sace mutum 5 a wani sabon hari a Sakkwato

[ad_1]



Aƙalla mutum biyar, ciki har da mata biyu masu juna biyu ’yan bindiga suka sace a ƙauyen Maiwa da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato.

Wani mazaunin ƙauyen ya ce ’yan bindigar sun shiga ƙauyen da misalin ƙarfe 5:10 na yammacin ranar Asabar, ɗauke da makamai a kan babura guda bakwai.

Ya ce sun isa lokacin da wasu mutane ke zaune a masallaci, inda suka harba bindiga sama domin tsoratar da jama’a.

Ya ce ya yi ƙoƙarin tserewa zuwa wajen ’yan sanda, amma su ma sun tsere bayan zuwa ’yan bindigar.

Daga nan ne ’yan bindigar suka shiga gidaje suka yi awon gaba da mutane.

An bayyana sunayen waɗanda aka sace da Sadiya Umar, Firdausi Umar, Maryam Musa, Ubaida Musa da Harira Nura.

Daga cikinsu, Sadiya Umar da Ubaida Musa na da juna biyu kuma suna daf da haihuwa.

’Yan bindigar sun kuma kwashe shanu 12 amma daga baya suka dawo da su.

Sun kuma doke wani mutum mai suna Malam Ya’u, wanda yanzu haka ake kula da shi a asibitin Sabon Birni.

Bayan harin, mazauna ƙauyen da dama sun tsere zuwa Jamhuriyar Nijar, amma sun dawo da safiyar ranar Lahadi.

Mazauna yankin sun buƙaci gwamnati da hukumomin tsaro su ƙara tsaurara matakan tsaro domin hana irin waɗannan hare-hare aukuwa a nan gaba.

Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin ’yan sandan jihar, DSP Ahmad Rufai, bai yi nasara ba domin bai amsa kira ko saƙon da aka aike masa ba har zuwa lokacin ha5da wannan rahoto.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *