Hukumar ‘Yansanda A Borno Ta Kwato Harsasai 912

[ad_1]

Hukumar ‘Yansanda ta Jihar Borno ta gano wani boyayyen tarin alburusai 912 nau’in B32 API (7.62 d 51mm) a yankin Kumshe Jamba Mari na birnin Maiduguri, babban birnin jihar.

Jami’in Hulda da Jama’a na ‘Yansanda na Jihar, ASP Nahum Daso, ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi cewa an tsare kayan cikin tsanaki yayin da bincike ke ci gaba don gano inda kayan suka fito da kuma makasudin amfani da su.

  • Yadda Dauda Lawal Ya Dukufa Wajen Farfado Da Darajar Jihar Zamfara
  • Dangote Ya Garzaya EFCC Da Ƙarar Tsohon Shugaban NMDPRA Bayan Janye Ta Daga ICPC

Sanarwar ta ce, “Hukumar ‘Yansanda ta Jihar Borno, karkashin jagorancin CP Naziru Abdulmajid, ta samu wani babban ci gaba a ayyukanta na tabbatar da tsaro da lafiyar jama’a a fadin jihar.

“A ranar 4 ga Janairu, 2026, da misalin karfe 2 na rana, Babban Jami’in Dansanda mai kula da Ofishin Lamisula Dibision, bisa bayanan sirri masu sahihanci, ya jagoranci tawagar ‘yansanda zuwa yankin Kumshe Jamba Mari, Maiduguri, inda aka gano boyayyun alburusai.”

“An kulle wurin cikin tsari na kwararru, inda aka kwato alburusai 912 na B32 API (7.62 d 51mm) cikin aminci. An tsare kayan da aka kwato yayin da bincike ke ci gaba don gano tushen kayan, makasudin amfani da su, da kuma kamo wadanda ke da alhakin lamarin,” in ji sanarwar.

Daso ya ce Kwamishinan ‘Yansanda, Naziru Abdulmajid, ya yaba wa jama’a kan bayar da bayanai cikin gaggawa da amfani, tare da sake jaddada cewa rundunar tana ci gaba da amfani da bincike bisa sirri wajen yaki da laifuka.

“Ya kara da cewa, jama’a su ci gaba da hadin kai da ‘yansanda ta hanyar bayar da rahoton duk wani motsi ko abin da ke da alamar shakku a cikin al’ummominsu,” in ji shi.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *