Rikicin Manoma Da Makiyaya: Gwamnatin Yobe Ta Kaddamar Da Rugar Fulani A Nguru
[ad_1]
Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe, ya kaddamar da rukunin Rugar Fulani a Karamar Hukumar Nguru.
Shahararren mai taimakon al’ummar nan, Alhaji Balarabe Abdullahi, wanda aka fi sani da Balarabe DJ ne ya kafa unguwar Ruga, domin rage tashin hankula a tsakanin manoma da makiyaya.
- GDPn Nijeriya Ya Yi Ƙasa Fiye da Na Shekaru 20 da Suka Wuce A Zamanin Obasanjo — Hashim
- Dabara Ta Rage Ga Mai Shiga Rijiya
Matsugunin yana da cikakkun kayan aikin zamantakewa da tattalin arziki, gami da gidaje masu daki biyu da kuma makaranta.
Sauran kayayyakin da aka samar sun hada da cibiyar kasuwanci, cibiyar kula da lafiya a matakin farko, samar da ruwan sha, wutar lantarki da kuma masallaci, duk an yi su ne domin tallafa wa makiyayan.
Yayin kaddamar da aikin, Gwamna Buni ya ce; shirin zai taimaka, wajen kawo karshen kiwo a fili, wanda a lokuta da dama yakan kai ga lalata gonaki.
Har ila yau, ya kuma yi nuni da cewa; samar da kiwo na zamani da ake yi a karkara, zai taimaka wa gwamnatin jihar wajen shigar da makiyaya cikin al’umma baki-daya tare da inganta harkar ilimi da kiwon lafiya.
Gwamnan ya kuma yi kira ga jama’a masu kishin kasa, da su yi koyi da irin yadda masu hannu da shuni ke tallafa wa zaman lafiya da ci gaba.
“Mun ga tasirin abubuwan da ya sanya a gaba da kuma alfanun da suke kawowa ga al’umma.
“Makaranta, dakin shan magani, asibiti da kuma gidajen da aka tanada, domin kasancewar Rugar, abin a yaba ne kwarai da gaske.
“Ya yi kyau, muna kuma godiya kwarai a madadin al’ummar Karamar Hukumar Nguru ta Jihar Yobe da Najeriya,” in ji gwamnan.
Tun da farko, Alhaji Abdullahi ya ce; an tsara shirin ne, domin rage tashe-tashen hankula a tsakanin makiyaya da manoma ta hanyar samar da wuraren kiwo.
[ad_2]
Source link