Tsohon Shugaban Asibitin Koyarwa na Katsina Bello Sulaiman ya rasu
[ad_1]
Tsohon Shugaban Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Katsina, Dokta Muhammad Bello Sulaiman, ya riga mu gidan gaskiya.
Majiyoyi makusantan iyalansa sun shaida cewa Dokta Bello Sulaiman ya rasu ne a ranar Asabar a wani asibiti da ke ƙasar Masar, bayan fama da jinya.
Tsohon Sanatan Katsina ta Arewa, Ahmad Babba Kaita, ya bayyana alhini kan rasuwar a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Sanatan ya bayyana marigayin a matsayin ƙwararren likita kuma jajirtacce mai kishin ci gaban Jihar Katsina.
“Innā lillāhi wa innā ilayhi rāji’ūn. Muna jimamin rasuwar Dokta Bello. Allah Ya jiƙansa, Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya sanya kyawawan ayyukansa su zama hujja a gare shi a Lahira,” in ji Babba Kaita.
Ya ƙara da cewa sha’awar marigayin wajen inganta harkokin lafiya a Katsina ta shahara matuƙa.
“Lokacin da nake Majalisar Tarayya kullum yana zuwa ofishina, yana zagayawa ba gajiyawa domin ganin an inganta harkokin lafiya a faɗin jihar,” in ji shi.
Ya kuma roƙi Allah Madaukakin Sarki da Ya sanya marigayin cikin Aljannar Firdausi.
Marigayi Dokta Bello Sulaiman ya shahara wajen bayar da gagarumar gudunmawa ga ci gaban harkokin lafiya a Jihar Katsina, musamman a lokacin da yake riƙe da muƙamin Shugaban Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Katsina.
A wani taro da aka gudanar a shekarar 2025 domin karrama shi bayan kammala wa’adinsa a matsayin shugaban asibitin, Ministan Lafiya, Muhammad Ali Pate, ya yaba wa Dokta Bello Sulaiman bisa sauye-sauyen da ya kawo a fannin lafiya.
Ministan, wanda a lokacin Dokta Abdulmajid Umar ya wakilta a yayin taron, ya ce marigayin ya aiwatar da tsare-tsare masu tasiri da suka taimaka wajen bunƙasa harkokin lafiya a jihar.
Aminiya ta ruwaito cewa rasuwar Dokta Muhammad Bello Sulaiman ta jefa al’ummar Katsina da ma fannin lafiya gaba ɗaya cikin jimami. Allah Ya gafarta masa, Ya sa Aljanna ta zama makomarsa.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link