Xi Ya Jagoranci Taron Shugabannin JKS Dangane Da Kiyaye Ka’idojin Jam’iyya Da Yaki Da Cin Hanci

[ad_1]

Ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya gudanar da taro a yau Alhamis, domin tattaunawa, da tsara ayyukan jam’iyyar kwaminis na bunkasa da’ar aiki, da gaskiya, da yaki da cin hanci na shekarar 2026 dake tafe. Taron ya gudana ne karkashin jagorancin babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping.

Yayin taron an amince cewa wajibi ne aikin sanya ido kan batun da’ar aiki, da sassan dake kula da hakan a shekarar 2026, su ingiza cikakken salon jagorancin kai bisa madaukakin matsayin inganci, kana su kara azamar aiwatar da nagartattun matakai, na wanzar da tabbaci ga cimma nasarar raya tattalin arziki da zaman rayuwar al’ummun kasar Sin, yayin da ake aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15 tsakanin shekarun 2026 zuwa 2030.

Har ila yau, an amince da gudanar da babban taron hukumar yaki da cin hanci ta JKS, tsakanin ranakun 12 zuwa 14 ga watan Janairun sabuwar shekarar 2026 dake tafe. (Mai fassara: Saminu Alhassan)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *