An ceto mutum 38 da aka sace a cocin Kwara — Tinubu
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewar an ceto dukkanin mutanen da mahara suka sace a wata coci a yankin Eruku na Jihar Kwara.
’Yan bindigar sun sace masu ibadar ne a ranar Talata, lokacin da suka kai hari cocin Almasihu na Cocin (Cac) da ke Oke Isegun a Eruku, wani gari da ke iyaka da Kogi a Karamar Hukumar Ekiti ta Jihar Kwara.
A cikin wani sako da Tinubu ya wallafa a X a ranar Lahadi, ya ce yana bibiyar yanayin tsaro a fadin kasar nan, kuma zai tabbatar da cewa gwamnatinsa ta kare ’yan Najeriya.
An yada bidiyon yadda maharan suka shiga cocin suka yi awon gaba da masu ibada yayin da suke tsaka da addu’a.
Lokacin da maharan suka dinga harbe-harbe a ciki cocin, wani Fasto ya jagoranci jama’a inda suka nemi mafaka.
Ya kuma ce an ceto dalibai 51 da aka sace a Jihar Neja.
Tinubu ya kara da cewa: “’Yan uwana ’yan Najeriya, za ku iya tuna cewa na soke zuwa taron G20 da aka yi a Afirka ta Kudu domin na mayar da hankali kan sha’anin tsaro a gida.
“Ina yi wa jami’an tsaro godiya kan aiki tukuru da suka cikin kwanaki biyun da suka wuce, an ceto dukkanin masu ibada 38 da aka sace a Eruku, a Jihar Kwara.
“Ina kuma farin ciki cewa an gano dalibai 51 daga cikin wadanda aka sace a wata makaranta a Jihar Neja.
“Ina bibiyar sha’anin tsaro sosai kuma ina samun rahotanni kai-tsaye. Ba zan yi kasa a gwiwa ba. Kowane dan Najeriya yana da ’yancin samun tsaro, kuma a karkashin jagorancina, za mu kare wannan kasa da mutanen ciki.”