Kano Pillars Ta Doke Enyimba, Ta Matsa Gaba A Teburin Gasar NPFL

[ad_1]

Ƙungiyar Kano Pillars ta doke Enyimba a gasar Firimiya ta Nijeriya ranar Lahadi. Chidozie Okorie da Ahmed Musa ne suka jefa ƙwallayen da suka yi sanadin nasarar.

Okorie ya buɗe ci a minti na 11 ga masu gida a filin wasa na Sani Abacha. Daga bisani Ahmed Musa ya ƙara ta biyu kafin a tafi hutun rabin lokaci.

  • Kano Pillars Ta Samu Nasarar Farko A Wasanni 8 Da Ta Buga
  • Kano Pillars Ta Fice Daga Jan Layi Bayan Doke El-Kanemi Warriors

Enyimba ta yi yunƙurin farke ƙwallaye amma ta ci tura. Tsauraran tsaron bayan Pillars ya hana su samun damar cin ƙwallo ko da guda.

Wasan ya ƙayatar da magoya bayan Kano Pillars sosai. Magoya bayan na fatan ƙungiyar za ta kammala kakar a matsayi mai kyau.

Wannan nasara ta ɗaga Pillars zuwa matsayi na 14 a teburin NPFL. Ƙungiyar na da maki 39 bayan buga wasanni 31.

Haka kuma, wannan ita ce ƙwallo ta huɗu da Ahmed Musa ya ci a kakar bana. Ita ce ta farko tun ranar 8 ga Maris.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *