Amnesty International Ta Zargi Jami’an Tsaron Uganda Da Azabtar Da Mutane
[ad_1]
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta zargi jami’an tsaron Uganda da azabtar da mutane da kuma kama su ba bisa ka’ida ba, yayin da kasar ke tunkarar zaben ranar 15 ga Janairu.
Shugaban kasar Yoweri Musebeni, mai shekara 81, na neman kara tsawaita mulkinsa na kusan shekaru 40, a daidai lokacin da ake zargin tsauraran matakai na kara tsananta domin murkushe ‘yan adawa.
Amnesty ta ce ta tattara shaidu da ke nuna jami’an tsaro na dukan masu zanga-zanga tare da harba hayakin mai hawaye kan magoya bayan jam’iyyar adawa ta National Unity Platform, wadda Bobi Wine ke jagoranta.
Bobi Wine, tsohon mawaki da ya koma siyasa, ya taba kalubalantar Musebeni a zaben 2021, wanda aka yi ta ce-ce-ku-ce kan sahihancinsa da kuma zargin amfani da karfin gwamnati wajen murda zaben.
Rahoton ya ce tashin hankali ya kara muni a ranar 28 ga Nuwamba, lokacin da aka kashe wani magoyin bayan NUP a wani gangami.
‘Yansanda sun ce suna tarwatsa taron da ya rikide zuwa tashin hankali, amma iyalan mamacin sun shaida wa Amnesty cewa an hana su halartar binciken gawar, kuma ba a ba su takardar shaidar mutuwa ba wadda ke nuna dalilin mutuwarsa ba.
Amnesty ta ce ta rubuta bayanan kama mutane kusan 400 daga cikin magoya bayan NUP a ‘yan watannin nan, inda da dama daga cikinsu suka bayyana cewa an doke su, an yi musu feshin barkonon tsohuwa, ko kuma an yi amfani da wutar lantarki a wajen azabtar da su.
Wani mutum ya ce an ja shi daga mota, sannan aka fesa masa barkonon tsohuwa kai tsaye a baki yayin wani gangami a Kampala.
Yayin da ranar zabe ke kara matsowa, ana nuna fargabar yiwuwar katse intanet, kamar yadda aka yi a 2021, ko da yake gwamnati ta musanta shirin yin hakan, amma ta gargadi cewa ba za ta lamunci yada tarzoma ko gudanar da gangamin da bai dace da doka ba.
[ad_2]
Source link