Shugabar Tanzania Ta Gana Da Wang Yi
[ad_1]
A yau Asabar ne ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da shugabar kasar Tanzania Samia Suluhu Hassan a birnin Dar es Salaam. Yayin zantawarsu, sun bayyana aniyar bai daya ta Sin da Tanzania, ta kara farfado da layin dogo da ya hada kasashen Tanzania da Zambia, a matsayinsa na ginshikin ingiza ci gaban tattalin arziki, kuma tushen samar da gajiya ga al’ummun sassan biyu.
A tsokacinsa, Wang ya ce kamata ya yi sassan biyu su hada kai wajen bunkasa hadin gwiwa mai matukar inganci, tare da kyautata layin dogon da aka farfado da shi zuwa jigon bunkasa ci gaban shiyyar, ta yadda zai zamo gadar kawance, da hanyar cimma gajiyar bai daya, wadda za ta wanzar da tarin alfanu ga al’ummun Tanzania, da ma sauran kasashen Afirka.
Har ila yau, Wang ya bayyana aniyar Sin ta yin aiki tare da Tanzania, wajen fadada musayar kwarewar jagoranci, da zurfafa hadin gwiwa na zahiri, da fadada musaya tsakanin al’ummun kasashen biyu, ta yadda sannu a hankali za a kai ga bunkasa cikakken kawance, bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Tanzania.
A nata bangare kuwa, shugaba Samia Hassan, cewa ta yi Tanzania a shirye take ta daidaita tsare-tsarenta na neman ci gaba tare da na Sin, da ingiza kara farfado da layin dogon na Tanzania zuwa Zambia, da habaka zirin samar da ci gaba kan turbar layin dogon.
Daga nan sai ta sake jaddada matsayar Tanzania, ta nacewa manufar nan ta Sin daya tak a duniya, tana mai jinjinawa manyan shawarwarin nan guda hudu na bunkasa ci gaban duniya da Sin ta gabatar. A daya bangaren kuma, shugabar ta ce kasarta ta shirya karfafa tsare-tsaren hadin kai a fannoni daban daban tare da Sin, kuma za su yi aiki tare wajen ingiza tsarin adalci, da daidaito domin cimma nasarar jagorancin kasa da kasa. (Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link