Yadda annobar tsutsa ta ja mana asarar miliyoyi — Manoman rake a Kano

[ad_1]



Manoman rake na Jihar Kano na fuskantar ɗaya daga cikin mafi munin barazana ga sana’arsu a ’yan shekarun nan, yayin da wata tsutsa mai hatsari ta mamaye gonakin rakensu a Karamar Hukumar Kura.

Annobar tsutsar wacce a Turanci ake kira Eldana saccharina, ta jefa ɗaruruwan manoma cikin asarar miliyoyin naira, sannan tana barazana ga rayuwar jama’a tare da tilasta wa matasa da dama barin noma don zuwa birane ci-rani.

Aminiya ta gano cewa tsutsar, wacce ke huda ke huda sandar rake da sauran amfanin gona, ta durƙusar da manoma a ƙauyukan irin su Dukawa, Kunshama, Ɗanga, Tofa, Kwari, Gamadan, Yadagungume, Tudu da Gidan Makera.

Manoman sun ce annobar ta kai matakin da ba a taɓa gani ba, inda gonaki gaba ɗaya suka lalace kuma raken ya koma kamar ya yi.

Noman rake dai na ɗaya daga cikin manyan hanyoyin samun kuɗin shiga ga al’ummomin Kura da makwabtanta, wanda iyalai da dama suka dogara da shi. Annobar tsutsar ba wai kawai ta lalata amfanin gona ba ne, har ma ta durƙusar da tattalin arziƙin yankin.

Manoma sun shaida wa Aminiya cewa asarar ta sa matasan yankin sun fara yin hijira zuwa birane don ci-rani.

Masana harkar noma sun yi gargaɗin cewa idan ba a ɗauki mataki ba, tsutsar za ta iya yaɗuwa zuwa sauran jihohin da ake noman rake, wanda hakan babbar barazana ce ga harkar samar da sukari a Najeriya.

Mun yi asarar ɗaruruwan miliyoyi sanadin tsutsar – Manoma

Ga Shehu Danga, wani manomin rake a Kura, lalacewar ta wuce duk yadda ake tunani.

“Ba mu taɓa asara mai munin wannan ba. A wasu gonakin, ba za mu iya girbe ko da sanda ɗaya ba; sai dai mu ƙone komai,” in ji shi.

Shehu ya ce ya yi asarar sama da miliyan shida a wannan shekarar, idan aka kwatanta da bara inda ya sayar da rake na sama da miliyan bakwai.

“Bana, ban sayar da ko ta miliyan ɗaya ba. Ban iya dawo da kuɗin taki da ban ruwa ba, balle ma na ’yan ƙwadago,” in ji Shehu.

Wani manomi, Hassan Ubale Shawai, ya ce ɓarnar tsutsar ta hana shi ciyar da iyalinsa.

“Noma ne kaɗai sana’armu a nan da muka gada tun iyaye da kakanni. Ni kaina na yi asarar sama da miliyan biyar a bana. Bara na sayar da rake na sama da N6.8m, amma bana ban samu ko ɗaya bisa ukun haka ba. Duk da faɗuwar farashin abinci a bana, amma da ƙyar nake iya ciyar da iyalina,” in ji shi.

Shi kuwa Sulaiman Adamu Tofa wanda shi ma manomi ne a yankin, ya ce ɓarnar tsutsar ta tilasta matasan yankin barin noma gaba ɗaya.

“Kusan komai ya lalace. Dole kana ji kana gani za ka cinna wa gonar wuta da kanka. Yanzu harkar ta durƙushe. Matasa da dama sun riga sun fara tafiya birane neman mafita,” kamar yadda ya bayyana.

Shi kuwa Dagacin Danhassan da ke yankin, Alhaji Aɗɗa’u Sani, ya shaida wa Aminiya cewa kusan dukkan al’ummomi maƙwabta suna dogaro da noman rake a matsayin babbar hanyar rayuwa a yankin.

Ya ce tsutsar ta katse musu hanyar rayuwa ɗaya tilo.

Himma Radio ta kawo ɗauki ga manoman

Gidan rediyon Himma, wanda shi ne rediyon al’umma na farko a Kano da ke mayar da hankali kan harkokin noma da abinci mai gina jiki, ya shirya taro inda ta haɗa manoma da masana daga Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK).

Tashar ta kuma kaddamar da asusun tallafi don tara agaji ga manoman da abin ya shafa.

Shugaban gidan rediyon, Ismail Yusuf Makwarari, ya ce matakin ya biyo bayan kiran da manoma na yankin suka yi musu.

“Bayan samun rahoton matsalar, mun haɗa manoman da Tsangayar Noma ta BUK don su yi bincike kan tsutsar su kuma bayar da mafita. Masana sun zo har ƙauyukan, suka ɗauki samfurin tsutsar, suka gano cewa Eldana saccharina ce,” in ji Makwarari.

‘Abin da muka gano game da tsutsar’

Dr. Baba Sani Wudil daga Tsangayar Noma a BUK, Sashen Kare Irin Shuka, ya tabbatar da cewa tsutsar samfurin Eldana saccharina ce.

Ya bayyana cewa tsutsar na huda jikin rake da sauran hatsi irin su dawa, gero, alkama, shinkafa da masara.

“Wannan tsutsa na da matuƙar illa, musamman a wuraren da ta kafa sansani. Kamar yadda na sani, Eldana saccharina ta daɗe a Najeriya duk inda ake noman rake,” in ji shi.

Dr. Wudil ya shawarci manoman da su rungumi dabarun yaƙi da ƙwari da tsutsotsi na zamani a gonakinsu.

“Manoma su kula da tsaftar gona da kuma sauya amfanin gona. Idan sun shuka rake a bana, su shuka kayan lambu a shekara mai zuwa. Wannan sauyawar za ta rage matsalar tsutsar,” in ji shi.

Ya ƙara da bayar da shawarar yin feshi da sinadarai tun farkon kakar da kuma amfani da magungunan kamar man darbejiya ko ganyenta ko ƙwayarta a gonakin.

“Yawan amfani da sinadarai barkatai na sa tsutsar ta saba da su har su daina yi mata tasiri. Shi ya sa nake ba da shawarar sauya sinadarai da dabarun gargajiya kamar sauya amfanin gona da magungunan feshi,” in ji shi.

Dr. Wudil ya jaddada cewa kawar da tsutsar zai buƙaci cikakken bincike, wanda zai iya kaiwa ga samar da nau’in rake mai jurewa.

“Mun sanar da Ma’aikatar Noma ta Tarayya ta hannun hukumar NRCI da Majalisar Rake ta Najeriya don su taimaka wa manoma. Maganin gaggawa shi ne kawo tallafin rage raɗaɗi ga manoman. Abu na biyu shi ne gwamnati ta zuba jari a bincike don samun magani na ƙarshe.”

Dr. Wudil ya jaddada cewa dabarun yaƙi da ƙwari da tsutsa tare da binciken gwamnati ne kaɗai mafita mai ɗorewa. “Muna buƙatar haɗin gwiwa tsakanin manoma, masana da masu tsara manufofi. Ba tare da kuɗi ba, bincike ba zai ci gaba ba. Idan ba a yi bincike ba, tsutsar za ta ci gaba da lalata gonaki,” kamar yadda ya yi gargaɗi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *