Ministan Hajji Da Umrah Na Saudiyya Ya Kawo Ziyarar Aiki Nijeriya

[ad_1]

Ministan Hajji da Umrah na Ƙasar Saudiyya, Dakta Tawfiq Al-Rabiah, ya iso Nijeriya a wata ziyarar aiki a hukumance, domin ƙarfafa haɗin guiwar da ke tsakanin Nijeriya da Ƙasar Saudiyya a fannin gudanar da ayyukan Hajji da Umrah.

Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, shi ne ya tarbi Ministan tare da tawagar jami’an Nijeriya, gabanin wata ganawa ta manyan jami’ai tsakanin ɓangarorin biyu.

  • Kashi 72 Na Ɗalibai Sun Lashe Jarabawar NECO Ta 2025
  • NDLEA Na Neman Al’umma Ta Goyi Bayan Shirye-shiryenta Na Yaƙi Da Noman Wiwi

A yayin ganawar, an mayar da hankali kan inganta tsare-tsaren Hajji da ƙarfafa haɗin kai da daidaito wajen shirye-shiryen tafiyar alhazai, da kuma inganta ayyukan hidima ga maniyyatan Nijeriya, tare da ƙarfafa daɗaɗɗIyar alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu.

Ana sa ran wannan ziyara za ta ƙara fahimtar juna, da kuma samar da ingantattun hanyoyin gudanar da aikin Hajji cikin sauƙi da walwala ga alhazai a kakar Hajji mai zuwa da ma shekarun gaba.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *