An kama wanda ake zargi da kashe kwarton matarsa a Yobe
[ad_1]
Rundunar ’yan sandan Jihar Yobe ta kama wani mutum mai shekaru 50, Hassan Umaru, bisa zargin kashe wani mutum da ake zargin kwarton matarsa ne.
Mai magana da yawun rundunar, SP Dungus Abdulkarim, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi a ƙauyen Bundila, da ke Ƙaramar Hukumar Gulani.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta bayyana cewa ana zargin Umaru ya kai wa mamacin, Sukari Abdul mai shekaru 45, hari da adda a kasuwar Bundila, inda ya ji mummunan rauni a wuyansa.
Sanarwar ta ce jami’an ’yan sanda daga ofishin Bara sun kai ɗauki cikin gaggawa bayan samun rahoton faruwar lamarin, inda suka garzaya da wanda aka jikkata zuwa Cibiyar Kula da Lafiya ta Matakin Farko da ke Bularafa domin ba shi agajin gaggawa, sai dai daga bisani ikitoci suka tabbatar da mutuwarsa.
“An kama wanda ake zargi nan take, tare da ƙwato addar da ake zargin an yi amfani da ita wajen aikata laifin.
“Daga nan aka miƙa lamarin ga Sashen Binciken Laifuka na Jiha (CID) domin gudanar da cikakken bincike,” in ji sanarwar.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Emmanuel Ado, ya gargaɗi al’umma da su guji ɗaukar doka a hannunsu wajen warware rikice-rikicen zamantakewa ko na aure.
Ya kuma buƙaci mazauna jihar da su riƙa kai ƙorafe-ƙorafensu ga hukumomin da suka dace, yana mai jaddada cewa rundunar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen gurfanar da duk wanda aka samu da laifi bisa tanadin doka.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link