PDP ta buƙaci a binciki kisan gillar Kwara
[ad_1]
Jam’iyyar PDP ta yi Allah-wadai da kisan da aka yi wa mutane sama da 100 a yankin Woro da ke ƙaramar hukumar Kaiama a Jihar Kwara.
A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Ini Ememobong ya fitar, ya buƙaci a gudanar da bincike cikin gaggawa kan abin da ta bayyana a matsayin gazawar tsaro da kuma yadda ake tafiyar da alamun gargaɗin tun kafin harin.
Ya ce, lamarin “wani abin tunatarwa ne game da yadda ’yan Najeriya ke fuskantar rashin tsaro a ƙarƙashin gwamnatin yanzu.”
Jam’iyyar PDP ta jajanta wa iyalan waɗanda abin ya shafa da mazauna al’ummar da abin ya shafa, tare da yin la’akari da iƙirari da shugabannin yankin suka yi na cewa an yi gargaɗin kai hari ba tare da abin da ta bayyana a matsayin matakan riga-kafi ba.
A cewar jam’iyyar, martanin da ya biyo bayan harin ya kasance mai “rauni ne da ya kamata a ɗauki mataki,” tare da jaddada bukƙatar yin nazari sosai kan ayyukan tsaro a yankin.
Jam’iyyar ta adawa ta buƙaci a kafa wani kwamiti mai zaman kansa da zai binciki al’amuran kashe-kashen da suka haɗa da rashin ɗaukar mataki kan gargaɗin da aka yi da wuri.
Haka kuma ta yi kira da a gaggauta samar da agajin jin ƙai, kula da lafiya da matsuguni na wucin gadi ga mutanen da suka rasa matsugunansu da waɗanda suka tsira a yankin Woro.
Duk da haka, Jam’iyyar PDP ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta kira taron gaggawa na tsaro na ƙasa wanda zai haɗa da masu ruwa da tsaki da kuma sanya hannun jari a cikin tsarin gargaɗin farko na al’umma don tabbatar da cewa, an magance sahihan barazana cikin gaggawa.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link