Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja
[ad_1]
Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya sauke Kwamishinan ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, Ajao Adewale, daga muƙaminsa.
Ko da yake ba a bayyana cikakken dalilin da ya sa aka sauke shi ba, majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa hakan ya faru ne sakamakon yadda rundunar Abuja, ta tafiyar da lamarin sanya gilishin mota mai duhu da kuma mutuwar ’yar jaridar gidan talabijin na Arise News.
Ɗaya daga cikin majiyoyin ta bayyana cewa waɗannan matsalolin guda biyu ne suka janyo sauya masa wajen aiki.
Ta ƙara da cewa za a tura Adewale wani waje daban, inda za a fi buƙatar ƙwarewarsa.
Da aka tambayi inda za a tura shi, majiyar ta ce Sufeton Janar na ’yan sanda ne zai bayyana hakan, tare da jaddada cewa Adewale ya yi iya bakin ƙoƙarinsa a matsayin kwamishina.
Kakakin rundunar ’yan sanda ta ƙasa, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da wannan sauyi, inda ya ce sauyin wajen aiki al’ada ce da ake yi domin inganta ayyukan jami’an rundunar.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link