NNPC Ta Rage Farashin Fetur

[ad_1]

Kamfanin man fetur na ƙasa (NNPC) ya rage farashin litar fetur a gidajen sayar da man fetur nasa zuwa N1,130 a Lagos da kuma N1,165 a Abuja.

Ragin farashin, wanda ya fara aiki ranar Laraba, ya nuna saukar N100 daga tsohon farashin N1,230 a Lagos, yayin da a Abuja kuma aka rage N95 daga N1,260 a lita.

  • Ƙungiyar PNGI Ta Yaba Wa Bayo Ojulari Bisa Nasarorin Gyare-gyare Da Aka Fara Samu A NNPC
  • Majalisar Dattawa Za Ta Gayyaci Kyari Kan Zargin Giɓin Kuɗi Har Naira Tiriliyan 210 A NNPCL

An lura da sabon farashin a wasu gidajen mai na NNPC da ke kan titin Isheri Oshun Road, Apple Junction da Ago Palace Way a Lagos, haka kuma a gidajen sayar da mai na kamfanin da ke yankunan Jabi da Wuse a Abuja.

Saukar farashin na zuwa ne duk da cewa wasu ‘yan kasuwar mai ba su fara aiwatar da sabon farashin da Matatar Dangote ta rage ba, inda matatar ta rage farashin ɗauka da N100 zuwa N1,075 a lita bayan faduwar farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya.

Rahotanni sun nuna cewa farashin ɗanyen mai ya fara sauka bayan yaƙin da ake yi a Gabas ta Tsakiya tsakanin Amurka, Iran da Israel. Haka kuma shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce rikicin na iya kawo ƙarshe nan ba da jimawa ba, abin da ya rage fargabar dagulewar samar da mai a duniya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *