Hotuna: Babbar Mota Ta Hallaka Wata Bafulatana A Bauchi
[ad_1]
Wani mummunan hatsari ya auku da misalin ƙarfe ɗaya na rana a ranar Alhamis, 29 ga Janairu, 2026, a ƙofar ATAP International School, kusa da shalƙwatar Hukumar Kula da Ilimin Firamare (SUBEB) ta Jihar Bauchi, a kan hanyar BACAS zuwa Awala, inda wata babbar mota ta hallaka wata Bafulatana mai sayar da fura da nono.
Wakilinmu, Khalid Idris Doya, wanda ya halarci wajen, ya ruwaito cewa ganau sun bayyana yadda wata motar ɗiban yashi (Tifa) ta yi ƙoƙarin fitowa bakin hanya ta baya, lamarin da ya sa wata babbar mota ta yi yunƙurin kaucewa domin guje wa karo da Tifar.
- ‘Yansanda Sun Cafke Mutum 2 Bisa Zargin Luwaɗi Da Ƙananan Yara A Bauchi
- Mazauna Bauchi Na Kokawa Kan Tsadar Farashin Acaba Duk Da Raguwar Farashin Mai
Sai dai a cikin wannan yunƙuri, wani ɗan achaba da ke ɗauke da Bafulatanar a mashin ya shiga tsakanin motocin, abin da ya janyo babbar motar ta faɗo a kan mashin ɗin tare da take matar, inda ta rasu nan take.

Jami’an Hukumar Kiyaye Haɗurra (FRSC) sun isa wurin da gaggawa, inda suka ɗauki gawar marigayiyar zuwa ɗakin adana gawarwaki na Asibitin ATBUTH, yayin da ake ci gaba da bincike kan ainihin musabbabin hatsarin.

[ad_2]
Source link