ECOWAS ta janye ragowar takunkuman da ta ƙaƙaba wa Guinea

[ad_1]



Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afrika (ECOWAS) ta janye duk ragowar takunkuman da ta ƙaƙaba wa ƙasar Guinea tun a shekarar 2021.

ECOWAS ta janye duk takunkuman da ta ƙaƙaba a dalilin juyin mulkin da aka yi a ƙasar kusan tsawon shekaru biyar da suka gabata, lamarin da ke tabbatar da dawowarta cikin harkokin ƙungiyar yankin.

An cimma wannan matsaya ne a ranar Laraba yayin taron shugabannin ƙasashe da gwamnatocin ECOWAS da aka gudanar a ƙasar Saliyo, bayan nasarar kammala tsarin miƙa mulki.

ECOWAS ta bayyana cewa an gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a ranar 28 ga Disamba, 2025, tare da rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar, Mamadi Doumbouya, bisa doka a farkon wannan wata.

A cewar ƙungiyar, nasarar gudanar da zaɓen da kuma rantsar da sabon shugaban ƙasar sun samar da yanayi mai kyau na dawo da dimokuraɗiyya, mutunta doka da oda, da kuma sake haɗa Guinea cikin harkokin yankin.

Tun da farko, ECOWAS ta dakatar da Guinea tare da ƙaƙaba mata takunkumi bayan juyin mulkin da sojoji ƙarƙashin jagorancin Mamadi Doumbouya suka yi, inda aka kifar da tsohon shugaban ƙasa Alpha Condé.

Sai dai a watan Fabrairun 2024, ECOWAS ta rage wasu daga cikin takunkuman, inda ta ɗage takunkumin mu’amalar kuɗi da cibiyoyinta.

Haka kuma, bayan nasarar kaɗa ƙuri’ar raba gardama kan kundin tsarin mulki a watan Satumba, da kuma zaɓen shugaban ƙasa a watan Disamba, ƙungiyar ta yanke shawarar ɗage dukkan sauran takunkuman nan take, har da waɗanda suka shafi mutanen da ke da hannu a juyin mulkin.

ECOWAS ta kuma mayar da Guinea cikakkiyar mamba a dukkan hukumomin yanke shawara na ƙungiyar tare da sauran ayyukan yankin, inda ta taya Shugaba Doumbouya murnar nasarar zaɓensa.

ECOWAS ta ƙarfafa wa Shugaba Doumbouya gwiwa da ya ci gaba da aiwatar da manufofin da za su ƙarfafa haɗin kan ƙasa, zaman lafiya, da ci gaban tattalin arziki domin amfanin al’ummar Guinea baki ɗaya.

Rahotanni sun nuna cewa bayan juyin mulkin 2021, gwamnatin Doumbouya ta fuskanci suka dangane da taƙaita ‘yancin faɗar albarkacin baki, hana zanga-zanga da kuma cafke ‘yan adawa, lamarin da ya sa wasu suka shiga gudun hijira.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *