Gidan rediyo ya ɗauki nauyin sanya yara 40 a makaranta a Kano

[ad_1]



Himma Radio, wani gidan rediyon al’umma da ke Jihar Kano, ya sanya yara 40 a makarantar firamare a ƙaramar hukumar Madobi.

An gudanar da bikin kaddamar da shirin ne a ranar Lahadi a harabar gidan rediyon da ke Madobi, da nufin rage yawan yara da ke gararamba a titunan jihar ba tare da zuwa makaranta ba.

Shugaban gidan rediyon, Ismail Yusuf Makwarari, ya ce wannan shiri wani ɓangare ne na aikin al’umma da gidan rediyon ke yi, kuma suna da burin faɗaɗa shi zuwa dukkanin ƙananan hukumomin jihar 44.

Ya ce, “Mu gidan rediyon al’umma ne da ke mayar da hankali kan harkar noma, kuma mun himmatu wajen inganta ci gaban yankunan karkara.

“Mun ƙaddamar da wannan shiri mai taken ‘Gangamin dawo da yara makaranta’ a matsayin wata hanya ta nuna cewa ilimi da noma su ne ginshiƙan ci gaba mai ɗorewa.”

Ya ƙara da cewa, “Mun zo da wannan tunani ne domin taimaka wa al’ummar da ke sauraron shirye-shiryenmu saboda Allah.

“A matsayina na shugaban kafar yaɗa labarai, mun ga cewa ba wai kawai mu riƙa fallasa matsalolin da ke cikin harkar ilimi ba ne, amma mu ma za mu iya taka rawa wajen kawo sauyi.”

Daga nan sai ya buƙaci sauran ƙungiyoyi da kamfanoni da su yi koyi da irin wannan aiki a matsayin gudummawarsu ga ci gaban ƙasa.

Hakimin Madobi kuma Majidadin Kano, Musa Saleh Kwankwaso, ya gode wa gidan rediyon bisa wannan hoɓɓasan da ya yi, tare da roƙon sauran masu hannu da shuni da su yi koyi da shi.

“Ilimi haƙƙin kowa ne, gwamnati ba za ta iya ɗaukar nauyin komai ita kaɗai ba. Irin waɗannan ƙungiyoyi da mutane su ma su shigo su taimaka. Muna farin ciki da wannan mataki da Himma Radio ta ɗauka,” in ji Hakimin.

Shugaban Jami’ar Bayero Kano (BUK), Farfesa Haruna Musa, wanda shi ma ya halarci bikin, ya ce Najeriya da ke da yawan jama’a sama da miliyan 200, waɗanda kuma fiye da rabinsu matasa ne, akwai buƙatar haɗa kai wajen tallafa wa fannin ilimi.

Ya kuma tabbatar da cewa ƙofar jami’arsa a buɗe take don haɗin gwiwa da duk masu ruwa da tsaki don ganin ta bunƙasa ilimi musamman a yankunan karkara.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *