Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 5 A Kebbi

[ad_1]

Dakarun Sojin Nijeriya sun kashe wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne su biyar bayan sun daƙile wani harin kwanton ɓauna a Jihar Kebbi.

Harin ya faru ne kusa da tsaunin Mayama lokacin da jerin motocin wani babban jami’in soja, Manjo Janar Bemgha Koughna, ke kan hanyarsa ta ziyartar sojoji a yankin.

  • Tinubu Ya Taya APC Murnar Nasara A Zaɓukan Birnin Tarayya, Kano Da Ribas
  • Zaben 2027: Jam’iyyun Siyasa Sun Bayyana Shirinsu Yayin Da INEC Ta Fitar Da Jawalin Zabe

Maharan da ake kyautata zaton Lakurawa ne suka buɗe wuta ba zato ba tsammani.

Sojojin sun mayar da martani cikin gaggawa inda suka fatattaki maharan tare da kashe biyar daga cikinsu.

Bayan fafatawar, sojoji sun binciki yankin tare da ƙwato makamai, alburusai, babura, wayoyi da kuma kuɗi.

Rundunar ta ce sojoji na ci gaba da zama a yankin domin hana sake kai wasu hare-hare da kuma kare jama’a.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *