Messi zai halarci ziyarar da Inter Miami za ta kai Fadar White House

[ad_1]



Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Inter Miami za ta kai ziyara White House a watan Maris domin bikin lashe gasar MLS ta shekarar 2025, inda ake sa ran fitaccen ɗan wasan Argentina Lionel Messi zai halarci taron.

Jaridar Miami Herald ta ruwaito cewa wani jami’in Inter Miami, wanda bai bayyana sunansa ba, ya ce “dukkan ’yan ƙungiyar” za su halarci bikin tare da Shugaban Amurka Donald Trump.

Rahoton ya ƙara da cewa ziyarar za ta gudana ne kwanaki biyu kafin Inter Miami ta fafata da DC United a birnin Washington ranar 7 ga Maris.

A watan Janairun 2025 ne Messi mai shekaru 38, ya samu lambar girmamawa mafi girma ta fararen hula a Amurka (Presidential Medal of Freedom) daga tsohon shugaban ƙasa Joe Biden, sai dai bai halarci bikin karramawar a White House a wancan lokaci ba.

Sha’awar Trump ga ƙwallon ƙafa ta ƙaru a ’yan watannin nan, inda ya yi taruka da shugaban Hukumar Ƙwallo ta Duniya (FIFA), Gianni Infantino, tare da karɓar baƙuncin tauraron ƙwallo, Cristiano Ronaldo a White House.

Trump ya kuma halarci bikin miƙa kofin Gasar Club World Cup da aka gudanar a Amurka a bara, haka nan ya halarci bikin fitar da jadawalin Gasar Kofin Duniya ta 2026, inda Infantino ya yi amfani da damar wajen ba shugaban Amurkan lambar yabo ta zaman lafiya ta FIFA karo na farko.

A ɓangaren wasanni, Inter Miami ta kammala jerin wasannin sada zumunci na kasa da kasa a ranar Alhamis da nasarar 2–1 kan Independiente del Valle a Puerto Rico.

Sai dai ƙungiyar ta sha kashi a wasan buɗe kakar MLS a hannun Los Angeles FC a ƙarshen makon da ya gabata, kuma ta doke Orlando City da ci 4-2 a ranar Lahadi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *