An sace Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukuma da Kansiloli 2 a Borno




Ana zargin ’yan Ƙungiyar ISWAP da sace sabon mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Biu da ke Borno, Alhaji Saidu tare da kansiloli biyu da wasu fasinjoji da dama.

Majiyar tsaro da ta mutanen garin Miringa, sun ce sacewar ta faru ne a ranar Laraba da yamma a kan hanyar ƙauyen Kamuya zuwa Buni Yadi yayin da waɗanda abin ya shafa ke tafiya zuwa Maiduguri bayan zaben ƙananan hukumomi da aka gudanar a ranar Asabar.

“Sabon mataimakin shugabanmu da aka zaba a zaben ƙananan hukumomi na ranar Asabar da ta gabata, Alhaji Saidu da Kansiloli biyu da ke wakiltar Zarawuyaku da Miringa na Ƙaramar hukumar Biu da ke jihar Borno, waɗanda ake zargin ‘yan Ƙungiyar ISWAP ne suka sace su tsakanin ƙauyen Kamuya da hanyar Buni Yadi,” in ji wani da ya buƙaci a sakaya sunansa.

Majiyoyin sun ƙara da cewa, maharan sun kuma kama wata motar Hisbah da ke tafiya da fito daga Potiskum, jihar Yobe, kuma suka sace mutanen cikinta tare da wata Motar Jama’atul Nasrul Islam (‘Yan Agaji) da ke kan hanyar zuwa Biu.

Ɗaya daga cikin kansilolin da aka sace shi ma tsohon mataimakin shugaban Ƙaramar hukumar Biu ne,” in ji majiyar.

Wani shugaban al’ummar Miringa da ba a bayyana sunansa ba, ya yi kira ne ga gwamnatin Jihar Borno da sojoji da sauran hukumomin tsaro da su ƙara himma wajen ceto sama da mutane 12 da aka kama daga dajin Sambisa.

Haka kuma, yankin Buni/Yadi-Miringa ya ci gaba da zama tarkon mutuwa, yayin da ‘yan Boko Haram da ISWAP suka sace masu ababen hawa, masu tafiya a ƙasa da manoma da yawan gaske a cikin shekaru bakwai da suka gabata.

Har zuwa kammala wannan rahoto babu wata majiya a hukumance da ta ce komai.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *