Gawuna ya ajiye mukamin da Tinubu ya ba shi na Shugaban Bankin Gidaje
[ad_1]
Dan takarar Gwamnan Jihar Kano na Jam’iyyar APC a zaben 2023, Nasiru Yusuf Gawuna, ya yi murabus daga mukamin da Shugaban Kasa Bola Tinubu ya nada shi na Shugaban Kwamitin Gudanarwa na Bankin Gidaje ta Kasa (FMBN).
Gawuna wanda shi ne Mataimakin Gwamnan Kano a wa’adin biyu na Abdullahi Umar Ganduje, daga 2015 zuwa 2023, ya dauki matakin ne a yayin da yake shirin sauya sheƙa zuwa Jam’iyyar ADC tare da jagoran Kwankwaasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Majiyoyi sun ce a ranar 27 ga Maris, 2026, Gawuna ya ajiye mukaminsa nan take. Hakan ya yi daidai da umarnin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ga masu rike da mukaman gwamnati da ke son tsayawa.
A halin yanzu dai zai yi aiki tare da tsohon jagoran NNPP na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso domin komawa ADC.
Wani kusa da tsohon mataimakin gwamnan ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa akwai rashin jin daɗi a tsakanin magoya bayan Gawuna kan yadda aka yi masa a APC duk da ya samu fiye da kuri’u 800,000 a zaben gwamna na baya.
Ya ce, “Magoya bayansa da dama suna matsa masa ya koma ADC. Duk da ya samu sama da kuri’u 800,000 a zaben da ya gabata, ba a ba shi wani muhimmin mukami ba. Jam’iyyar ta yi masa rashin adalci.”
Ana kallon sauya shekar Gawuna a matsayin wani ɓangare na sabon tsarin siyasa a Kano, inda ADC ke ƙoƙarin zama sabuwar ƙarfi a gaban zaben 2027.
Yau Litinin ake sa ran Kwankwaso zai koma APC, wanda hakan zai buɗe hanya ga shigar Gawuna gobe Talata.
Masu lura da siyasa sun ce wannan sauyi na iya raunana APC a Kano—jiha mai muhimmanci a siyasa—tare da ƙarfafa Kwankwasiyya a fafatawar gaba da Gwamna Abba Kabir Yusuf a zagayen zabe na gaba.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link