Jami’ar Skyline ta horas da ‘yan jarida kan dabarun jagoranci

[ad_1]



Jami’ar Skyline da ke Kano ta shirya wani taron yini huda domin horas da ma’aikatan jarida da masu hulɗa da kafofin yaɗa labarai kan dabarun shugabanci mai inganci da hangen nesa.

Shirin horaswar, wanda aka gudanar a ɗakin taro na Rabiu Musa Kwankwaso da ke harabar jami’ar a Kano, ya mayar da hankali ne kan yadda ‘yan jarida za su inganta ƙwarewarsu a fannin jagoranci, yanke shawara da kuma sarrafa bayanai cikin hikima.

Masu gabatar da laccoci a taron sun jaddada muhimmancin shugabanci mai haɗe da zurfin tunani, musamman a wannan zamani da ke fuskantar sauye-sauye a harkokin yaɗa labarai.

Shugaban jami’ar, Farfesa Ajith Kumar V.V, yana bayar da horo

Yadda ma’aikatan jarida ke samun horo

Shugaban jami’ar, Farfesa Ajith Kumar V.V wanda shi ne jagoran masu horaswar, ya fara ne da buga misalai da wasu fitattun mutane a duniya da suka zamo zakaran-gwajin dafi wajen kawo muhimman sauye-sauyen a fannonin da suka sa a gaba, musamman la’akari da riƙon da suka yi wasu aƙidun jagoranci nagari masu nasaba da tabbatar da nasara.

Ya bayar da misalai da mutanen da suka yi fice a fagen jagoranci da kuma samun nasara a rayuwa kamar mu’assasin kamfanin Apple, marigayi Steve Jobs, tsohon Firaministan Singapore, Lee Kuan Yew, Darwin Smith da sauransu.

Wasu daga cikin mahalarta taron sun bayyana cewa sun amfana da shirin, inda suka ce zai taimaka musu wajen inganta aikinsu da kuma yadda suke tafiyar da harkokin sadarwa.

Jami’ar ta bayyana cewa za ta ci gaba da shirya irin wannan horo domin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ta da masu aikin jarida, tare da bunƙasa ƙwarewar su a fannin sadarwa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *