Ana zargin jami’in sibil difens da harbe abokin aikinsa a Abuja
Iyalan wani jami’in sibil difens mai suna DSP Adama Adekunle Emmanuel mai shekaru 45, sun ce suna zargin wani abokin aikinsa ya harbe shi har lahira a ranar Lahadi.
Mai ɗakin margayin ta yi iƙirarin lamarin ya faru ne a wani Otel da ke Abuja, tana mai cewa alamu sun nuna kashe mijin nata aka yi, saboda raunukan harbin bindiga da suka gani a kafaɗunsa.
Sai dai ta ce suna zargin wasu na ƙoƙarin lulluɓe zancen, kasancewar labarai daban-daban har kashi uku masu cin karo da juna aka ba su kan sanadiyyar mutuwarsa.
Kakakin rundunar ’yan sandan Birnin Tarayya, Josephine Adeh, ta ce suna nan suna bincike domin gano haƙiƙanin abin da ya faru.