Mutum 2 sun mutu, 10 sun jikkata a Gombe

[ad_1]



Hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa FRSC ta tabbatar da mutuwar mutane biyu tare da jikkatar wasu 10 a wani hatsarin mota da ya afku a kan hanyar Gombe zuwa Yola.

Hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:40 na yammacin ranar Juma’a a yankin Gona, inda rahotanni suka nuna cewa fashewar taya ce ta haddasa shi.

Kwamandan FRSC na jihar, Mista Samson Kaura, ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai, yana mai cewa hatsarin na mota guda ɗaya ne.

Ya ce mutanen da suka jikkata sun samu raunuka iri-iri da suka haɗa da na kai, kurjewa da sauransu.

A cewarsa, an garzaya da waɗanda suka samu raunuka zuwa Asibitin Koyarwa na Tarayya domin samun kulawar likitoci, yayin da aka kai gawarwakin waɗanda suka rasu ɗakin ajiye gawa na asibitin.

Ya ƙara da cewa binciken farko ya nuna fashewar taya ce ta janyo hatsarin, wanda ka iya nasaba da tuƙin ganganci, ɗaukar kaya fiye da ƙa’ida ko gudun wuce ƙima.

Kaura ya yi kira ga direbobi da su kiyaye dokokin hanya, su guji lodin da ya wuce ƙima da kuma gudun wuce sa’a, yana mai jaddada muhimmancin tsaron rayuka.

“Dole ne direbobi su fifita lafiyarsu da ta fasinjoji fiye da gaggawa ko neman riba, domin iyalansu na jiran dawowarsu lafiya,” in ji shi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *