’Yan sanda 4 sun mutu a harin ’yan ta’adda a Borno
[ad_1]
Aƙalla jami’an ’yan sanda huɗu da wani mafarauci ɗaya sun mutu a wani hari da ake zargin mayaƙan Boko Haram da ISWAP ne suka kai a wasu yankuna na Jihar Borno.
Mai magana da yawun ’yan sanda a jihar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da tsakar dare a ƙananan hukumomin Nganzai da Mobbar.
Ya ce a ranar Asabar, 4 ga Afrilu da misalin ƙarfe 1:00 na dare, ’yan ta’addan suka kai hari hedikwatar ’yan sanda ta Nganzai da zummar ƙwace garin.
Sai dai ya ce jami’an ’yan sanda tare da haɗin gwiwar rundunar MOPOL da kuma ƙungiyar Crack Squad sun fafata da maharan a wani gumurzu, inda suka daƙile harin tare da hana su shiga garin.
Haka kuma, ya ce maharan sun yi amfani da manyan makamai ciki har da rokoki, lamarin da ya janyo lalata wani ɓangare na ofishin ’yan sanda har da ƙona wata tsohuwar motar sulke.
“Amma abin takaici, jami’an ’yan sanda huɗu sun rasa rayukansu a bakin aiki,” in ji shi.
A wani hari makamancin haka da ya faru da misalin ƙarfe 2:40 na dare a ranar Asabar, ’yan ta’adda sun kai farmaki sansanin ’yan gudun hijira na Malam Fatori da ke Damasak a Ƙaramar Hukumar Mobbar.
Rahoton ya ce maharan sun nufi wurin sintiri na haɗin gwiwar CJTF da mafarauta a ƙofar sansanin, inda wani mafarauci mai suna Atom Abua mai shekara 40 ya rasa ransa.
Haka kuma, an yi asarar gidaje kusan 20 da rumfunan ƙasa a sakamakon harin.
ASP Daso ya ƙara da cewa an daƙile harin yayin da haɗin gwiwar jami’an tsaro da suka haɗa da ’yan sanda, sojoji, CJTF da mafarauta suka tari hanzarin cikin gaggawa.
Ya ce Kwamishinan ’yan sanda na jihar, CP Naziru Abdulmajid, ya aika da ƙarin jami’ai da kayan aiki zuwa wuraren domin ƙarfafa tsaro da kuma hana sake aukuwar irin wannan lamari a nan gaba.
Ya kuma yaba da jarumtar jami’an da suka fuskanci maharan, yana mai miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu.
“Hukumar za ta ci gaba da farautar waɗanda suka aikata wannan aika-aika domin gurfanar da su a gaban kotu,” in ji shi.
Ya buƙaci jama’a da su kwantar da hankalinsu, su kasance masu lura, tare da bai wa jami’an tsaro cikakken haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link