Sin Ta Kaddamar Da Shirin “Operation Sky Net 2026” Don Taso Keyar Masu Cin Hanci Da Suka Tsere
[ad_1]
A yau Alhamis, ofishin taso keyar masu laifi da suka tsere tare da kwato kadarori na tawagar tsara yaki da cin hanci da rashawa ta gwamnatin tsakiya ta kasar Sin, ya sanar da kaddamar da shirin “Operation Sky Net 2026,” wani shiri da ke mai da hankali kan taso keyar masu cin hanci da rashawa da suka tsere da kuma kwato dukiyoyin da aka samu ta haramtacciyar hanya.
An fara kaddamar da shirin na “Operation Sky Net” ne a shekarar 2015.
A cewar ofishin, shirin na shekarar 2026 zai kunshi sassa daban-daban da za su hada karfi da karfe cikin tsari domin kwato haramtattun dukiyoyin da aka samu ta hanyoyin miyagun laifuffukan da suka shafi aiki, da bin sawun masu laifuka na tattalin arziki da suka tsere zuwa kasashen waje, da dakile tura kudaden haram zuwa kasashen waje ta hanyar kamfanonin ketare, da bankunan boye, da kuma magance matsalar jami’an gwamnati da iyalansu ke zaune a kasashen waje. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link