An ba da tallafin N2m ga iyalan jami’in NSCDC da aka kashe a Jigawa
[ad_1]
Gwamnatin Jihar Jigawa ta bayar da tallafin Naira miliyan biyu ga iyalan SC Bashir Adamu Jibrin, jami’in hukumar sibil difens (NSCDC) da ya rasu a bakin aiki a kasuwar Shuwarin da ke ƙaramar hukumar Kiyawa.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Bala Ibrahim, ne ya miƙa tallafin ga matar marigayin a ofishinsa, inda ya ce wannan taimako na nufin tallafa wa iyalan marigayin tare da taimaka musu wajen kula da tarbiyyar ’ya’yansu.
Ya shawarci matar marigayin da ta yi amfani da kuɗaɗen wajen kula da ilimi da walwalar ’ya’yanta, tare da jaddada cewa gwamnatin Jigawa za ta ci gaba da girmama sadaukarwar jami’an tsaro da ke bayar da rayukansu don kare al’umma.
Da yake martani, Kwamandan NSCDC na Jihar Jigawa, Muhammad Kabir Ingawa, ya gode wa gwamnatin jihar bisa wannan alheri, yana mai roƙon Allah ya jiƙan marigayin.
Ita ma a nata ɓangaren, matar marigayin, Zainab Muhammad Ahmed, ta bayyana godiyarta ga gwamnatin jihar bisa wannan taimako, tare da tabbatar da cewa za ta yi amfani da kuɗaɗen yadda ya dace.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link