Gwamnatin Ghana Ta Sake Buɗe Matatar Man Fetur Bayan Rufe Ta A Baya

[ad_1]

Gwamnatin Ghana ta sake farfaɗo da matatar man fetur mallakin ƙasar wadda aka rufe a 2021 sakamakon wasu matsalolin da suka dabaibaye ta.
Matatar an gina ta ne a shekarar 1960, inda take zaman kanta amma an dawo da ita ƙarƙashin kulawar gwamnati a 1977.
Matatar, tana da karfin fitar da ganga 28,000, amma gwamnatin na fatan ɗaga wannan adadin zuwa ganga 45,000 nan ba da jimawa ba.
Ana kyautata zaton cewa, basussuka, tashin farashin ɗanyen mai a duniya, tsadar canjin kuɗaɗen ƙetare da kuma rashin jagoranci, na daga cikin manyan dalilan da suka sanya rufe matatar a baya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *