Mutane 17 sun mutu a hatsarin mota a Jigawa
[ad_1]
Mutane 17, ciki har da kananan yara, sun mutu a wani hatsarin mota a garin Danmasara da ke Karamar Hukumar Dutse, Jihar Jigawa.
Hukumar Kiyaye Lafiyar Hanya ta Kasa (FRSC) ta bayyana cewa hatsarin ya faru ne a kan hanyar Dutse-Kwanar Huguma, ranar Talata da misalin ƙarfe 12:15 na rana, inda ya rutsa da motoci uku — motoci biyu kirar Volkswagen Golf da kuma wata tifa kirar Marsandi.
Mai magana da yawun FRSC a jihar, CRC YI Yahaya, ya ce an samu rahoton hatsarin da misalin ƙarfe 12:17 na rana, sannan jami’an ceto suka isa wurin da misalin 12:23 na rana.
Binciken farko ya nuna cewa gudun wuce gona da iri, fashewar tayar mota, da rasa kwacewar mota ne suka jawo wannan mummunan hatsari.
“A hatsarin nan, mutane 17 sun mutu, ciki har da manya da yara,” in ji sanarwar, ta ƙara da cewa an kwashe waɗanda suka jikkata da kuma gawarwakin zuwa Asibitin Kwararru Dutse domin kulawar gaggawa da kuma yin rajista.
FRSC ta Jihar Jigawa ta yi gargadi ga direbobi da su guji gudun wuce gona da iri da kuma sakaci wajen kula da motocinsu, musamman tayoyi.
Ta kuma yi kira ga masu amfani da hanya da su rika bin ƙa’idojin zirga-zirga domin kauce wa asarar rayuka da za a iya kaucewa.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link