‘Yan Bindiga Sun Sace Matafiya A Benue Da Kogi
[ad_1]
‘Yan bindiga sun sace wasu matafiya a wasu hare-hare daban-daban da suka kai a jihohin Benue da Kogi.
Sun kashe wasu, wasu kuma sun jikkata, yayin da jami’an tsaro suka fara ƙoƙarin ceto waɗanda aka sace.
- Kasar Sin Ta Dade Tana Zama Aminiya Kuma ’Yar Uwa Ga Kasashen Afirka
- Kamfanin Matatar Man Fetur Na Dangote Ya Rage Farashin Mai Zuwa ₦774
A Jihar Benue, maharan sun kai hari kan wata motar haya a kan hanyar Utonkon–Okpoga a yammacin ranar Litinin.
Motar na ɗauke da fasinjoji 16 daga ƙananan hukumomin Oju da Obi.
‘Yan bindigar sun tare motar tare da awon gaba da fasinjojin zuwa cikin daji.
Shugabannin yankin sun ce an kashe mutum biyu, an kuma ceto mutum biyu, yayin da sauran 12 ke hannun maharan.
Jami’an tsaro na ci gaba da neman su.
A Jihar Kogi kuma, wasu da ake zargin masu garkuwa ne sun kai hari kan motoci uku a kan hanyar Ejule–Alloma a ƙaramar hukumar Ofu.
Motocin na kan hanyarsu ta zuwa Enugu lokacin da maharan suka tare hanya suka buɗe musu wuta.
Majiyoyin tsaro sun ce an sace fasinjoji huɗu daga ɗaya daga cikin motocin, yayin da wasu suka tsira da raunukansu.
An ceto ɗaya daga cikin waɗanda aka sace, kuma tana asibiti ana kula da ita.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ‘yansanda a jihohin biyu ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba.
[ad_2]
Source link