Tinubu zai halarci bikin kamun kifi na Argungu na bana – Gwamnan Kebbi

[ad_1]



Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya tabbatar da cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu zai halarci bikin kamun kifi na Argungu na bana.

Gwamnan ya bayyana hakan a Birnin Kebbi, inda ya ce bikin na ci gaba da jan hankalin manyan mutane da shugabanni daga sassa daban-daban na Afirka.

A cewar Gwamnan, bikin da za a gudanar ranar Asabar zai kasance dama ta musamman ga mutanen jihar, domin Shugaban Ƙasa zai ƙaddamar da wasu ayyuka tare da halartar bikin.

“Ina tabbatar wa mutanen Kebbi cewa Shugaban Ƙasa zai zo jiharmu a wannan makon don ƙaddamar da ayyuka da kuma halartar bikin kamun kifi. Wannan wata dama ce ga mutanenmu,” in ji shi.

Ya yi kira ga al’ummar jihar da su fito da yawansu domin tarbar Shugaban a ranar Asabar.

Bikin kamun kifi na Argungu karo na 61 zai gudana na tsawon kwana huɗu daga ranar Laraba zuwa Asabar mai zuwa.

A nasa jawabin, Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kebbi, Alhaji Yakubu Ahmed BK, ya nemi afuwar jama’a kan rufe wasu hanyoyin mota a Birnin Kebbi da kuma garin Argungu a ranar Asabar saboda tsaro da gudanar da bikin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *