Allah zai kunyata masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Zamfara — Gwamna Dauda

[ad_1]



Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara, ya ziyarci wasu garuruwa a Ƙaramar Hukumar Kauran Namoda, bayan jerin hare-haren ’yan bindiga da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Gwamnan, ya la’anci kisan gillar, tare da bayyana shi a matsayin marasa imani, kuma Allah zai fallasa su ya kunyata su.

A ranar Laraba, ya ziyarci ƙauyuka biyar da abin ya fi shafa; Banga, Sakajiki, Kuryar Madaro, Maguru, da Tambarawa, inda mutane da dama suka rasa ’yan uwansu.

Bayan samun labarin hare-haren, nan da nan ya tura mataimakinsa ya je ya jajanta wa mutanen da abin ya shafa.

Bayan dawowarsa Gusau, ya je da kansa ya duba ɓarnar da aka yi tare da yi wa iyalan mamatan ta’aziyya.

Ya bayyana maharan a matsayin maƙiyan zaman lafiya da ke son haifar da tsoro da rikice-rikice, sannan ya roƙi jama’a su ci gaba da addu’a don kawo ƙarshen aikata laifuka a jihar.

Gwamnan, ya yi alƙawarin ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ’yan bindiga ta hanyar amfani da sabbin dabaru da ƙarfafa haɗin gwiwa.

Sarkin Kauran Namoda, Dakta Sunusi Ahmad, ya yaba wa gwamnan bisa ziyarar da ya kai, inda ya bayyana cewa hakan ya ƙarfafa guiwar mutanen yankin.

Haka kuma, Gwamna Lawal, ya sanar da shirin inganta rayuwar jama’a ta hanyar gyaran hanyoyi, samar da wutar lantarki, ruwan sha, da inganta sadarwar wayar salula a yankin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *