Salah zai bar Liverpool a ƙarshen kaka
[ad_1]
Fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Masar, Mohamed Salah, ya sanar da cewa zai bar Liverpool FC a ƙarshen kakar wasan 2025/2026, bayan kusan shekaru tara da ya shafe a kulob ɗin.
Salah, mai shekaru 33, ya bayyana hakan ne a wani bidiyo da ya wallafa a kafafen sada zumunta, inda ya ce lokaci ya yi da zai yi bankwana da kulob ɗin da ya bayyana a matsayin “gida”.
Tun bayan zuwansa daga AS Roma a 2017, Salah ya buga wasanni 435, inda ya zura ƙwallaye 255, lamarin da ya sa ya zama na uku cikin waɗanda suka fi zura ƙwallaye a tarihin Liverpool bayan Ian Rush da Roger Hunt.
A tsawon zamansa, ya lashe manyan kofuna ciki har da gasar Premier League sau biyu (2019/20 da 2024/25), da kuma UEFA Champions League a 2019.
Haka kuma, Salah yana da kambin nasarar lashe wasu gasannin kamar FA Cup, League Cup, Club World Cup da UEFA Super Cup.
Sai dai kakar bana ta kasance mai rauni a gare shi, inda ya zura ƙwallaye biyar kacal a gasar Premier League, sabanin 29 da ya ci a kakar da ta gabata.
Makomar Salah a kulob ɗin ta kasance cikin cece-kuce tun bayan saɓaninsa da koci Arne Slot a watan Disamba, inda ya zargi kulob ɗin da rashin goyon baya bayan an ajiye shi a benci sau uku a jere.
A saƙon bankwanarsa, Salah ya gode wa magoya baya da abokan wasansa, yana mai cewa ba zai taɓa mantawa da goyon bayan da suka ba shi ba a lokacin da ya fi haskawa da kuma lokacin ƙalubale.
Kulob ɗin Liverpool ya kuma bayyana cewa Salah zai kammala “babban tarihi mai ɗauke da nasarori” a Anfield, yayin da ake sa ran zai yi ƙoƙarin barin kulob ɗin da wata babbar nasara, musamman a gasar Champions League.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link