Sashen Kera Jiragen Ruwa Na Kasar Sin Ya Ci Gaba Da Zama Kan Gaba A Duniya A 2025

[ad_1]

Masana’antar kera jiragen ruwa ta kasar Sin ta ci gaba da rike kaso mafi girma a kasuwar duniya bisa manyan ma’aunai guda uku a cikin shekaru 16 a jere zuwa shekarar 2025, kamar yadda alkaluman da ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar ta fitar a yau Lahadi suka nuna.

Yawan jiragen ruwan da kasar ta samar ya kai tan miliyan 53.69 a ma’unin nauyi na DWT a shekarar 2025, wanda ya karu da kashi 11.4 cikin dari a shekarar, kuma ya kai kashi 56.1 cikin dari na jimillar wadanda aka samar a duk fadin duniya.

Sabbin odar da aka bayar sun kai tan miliyan 107.82 a ma’aunin DWT a bara, wanda ya nuna kashi 69 cikin dari na kasuwar duniya a bangaren.

Ya zuwa karshen Disambar shekarar 2025, odar da ba a kammala ba a sashen ya kai tan miliyan 274.42 a ma’unin DWT, wadda ta karu da kashi 31.5 cikin dari idan aka kwatanta da ta shekarar 2024. Wannan adadin ya kai kashi 66.8 cikin dari na kasuwar duniya a bangaren. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *