Jirgin sama ya yi hatsari yayin sauka a Kano

[ad_1]



Wani jirgin sama mallakin kamfanin Flybird, ya yi hatsari yayin sauka a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano.

Jirgin ya taso daga Abuja, kuma lamarin ya faru ne a lokacin da yake ƙoƙarin sauka a filin jirgin saman Kano, a ranar Lahadi.

Majiyoyi daga filin jirgin saman, sun bayyana cewa babu wani fasinja ko ma’aikacin jirgin da ya ji rauni.

Wani jami’in filin jirgin ya shaida wa Aminiya, cewa hukumomin sufurin jiragen sama ko Hedikwatar Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Tarayya (FAAN) ne, kaɗai za su iya yin ƙarin bayani kan lamarin.

Wata majiya kuma ta tabbatar da cewa fasinjoji 11 ne ke cikin jirgin a lokacin da lamarin ya faru.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *