Yadda aka horar da mata 100 sana’o’in dogaro da kai a Gombe

[ad_1]



Cibiyar HANs Centre for Social Justice and Development tare da Kanady Academy, sun kammala horon kwana uku domin koya wa yara marasa galihu da matasa mata sana’o’in dogaro da kai a Jihar Gombe.

Shugabar HANs, Barista Hannatu Dauda Simon, ta ce an shirya horon ne domin ƙarfafa gwiwar mahalarta, tare da koya musu yadda za su iya rayuwa ba tare da dogaro da wasu ba.

Ta ce halin tattalin arziƙin ƙasar nan ya ƙara nuna muhimmancin sana’ar hannu ga matasa.

Ta bayyana cewa matasa mata 100, ciki har da ɗaliban Kanady Academy ne, suka halarci horon.

Masu horarwa daga fannoni daban-daban sun koya wa matasan sana’o’i kamar:

– Yin takalmi

– Yin burodi

– Kwalliya

– Turaren wuta

– Sarrafa kilishi

– Kula da shagunan kaya

– Da sauran sana’o’in dogaro da kai.

Ta yaba da yadda mahalarta suka dage a lokacin horon, tana mai cewa za su yi baje kolin abin da suka koya nan gaba domin nuna ƙwarewarsu.

Ta kuma ce ilimin da aka ba su zai taimaka musu wajen samun abin dogaro da kai.

Wasu daga cikin mahalartan sun bayyana farin cikinsu, inda suka bayyana cewa horon ya taimaka musu gano sana’ar da ta dace da su.

Haka kuma sun yi godiya kan kayan aikin da aka ba su domin su fara ƙananan sana’o’i.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *