Shettima Ya Dawo Nijeriya Bayan Halartar Taron G20 Da AU–EU

[ad_1]


Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya dawo Abuja daga birnin Luanda a Angola, inda ya halarci taron AU–EU karo na 7 a madadin Shugaba Bola Tinubu.

Ya wakilci shugaban ƙasa a taron G20 na 2025 da aka yi a Johannesburg, Afirka Ta Kudu.

A Angola, Shettima ya karanta saƙon Shugaba Tinubu wanda ya sake jaddada buƙatar Afrika na samun kujerun dindindin da ikon zartarwa a Majalisar Ɗinkin Duniya.

Ya kuma buƙaci Tarayyar Turai su haɗa kai da Afrika wajen samar da tsare-tsaren zaman lafiya da tsaro.

Shugaba Tinubu ya kuma tabbatar da ƙudirin Nijeriya na ci gaba da inganta zaman lafiya, tsaro da mulki na gari a Afrika, tare da yin aiki da Tarayyar Turai domin samun daidaito da kwanciyar hankali.

A taron G20 da aka yi a Afirka Ta Kudu, Tinubu ya buƙaci shugabannin duniya su samar da tsarin kuɗi na ƙasa da ƙasa, tare da magance matsalolin bashi.

Ya ce tsarin da ake amfani da shi a yanzu ya zama tsohon yayi kuma bai dace da ƙalubalen wannan zamani ba.

Tinubu ya kuma nemi a samar da ƙa’idojin duniya da za su tabbatar da cewa ƙasashen da ke samar da muhimman ma’adanai ciki har da Nijeriya, suna amfana da su.

Haka kuma, ya goyi bayan samar da ƙa’idojin amfani da fasahar Artificial Intelligence (AI) domin ci gaban duniya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *