Sheikh Gumi Ya Maka Wasu Mutum 2 A Kotu Kan Zargin Ɓata Masa Suna

[ad_1]

Fitaccen Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya maka wasu masu amfani da Facebook su biyu kotu kan zargin yi masa barazana da ɓata masa suna.

Ya zargi George Udom da Bello Isiaka da wallafa wani saƙo a Facebook da ya bayyana cewa ya yi barazana ga Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (ritaya).

  • AFCON 2026: Algeria Ta Lallasa Sudan Da Ci 3 Da Nema
  • Yadda Ake Inganta Tsarin Harkokin Kudi Na Dattawa A Kasar Sin

Sheikh Gumi ya ce bai taɓa faɗin wannan magana ba kuma ya bayyana saƙon a matsayin hatsari kuma zai ɓata masa suna.

Ya shigar da ƙarar a ranar 24 ga watan Disamba, 2025, kuma lauyoyin Sheikh Gumi sun ce saƙon ya kuma danganta malamin a matsayin mai goyon bayan ta’addanci.

Sheikh Gumi, wanda aka sani da koyar da zaman lafiya da sulhu, ya ce saƙon zai iya jefa rayuwarsa cikin hatsari.

Lauyoyinsa sun yi gargaɗin cewa amfani da kafafen sada zumunta wajen yaɗa labaran ƙarya babban laifi ne.

Lauyoyin sun ce ƙarar na nufin zama gargaɗi ga duk wanda zai wallafa ko yaɗa bayanan da ba a tabbatar da su ba.

Sheikh Gumi ya yi kira ga masu amfani da kafafen sada zumunta da su tabbatar da gaskiyar bayanai kafin su yaɗa su, yana mai jaddada cewa yaɗa ƙarya na iya haifar da manyan matsaloli game da tsaro.

Ya ce kare sunan mutum da yaɗa gaskiya yana da matuƙar muhimmanci a Intanet.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *