Tinubu Ya Kafa Kwamiti Don Warware Rikicin APC Kafin Zaɓen 2027
Shugaba Bola Tinubu ya kafa wani kwamiti da zai warware rikice-rikice a cikin jam’iyyar APC kafin tunkarar zaɓen 2027.
Kwamitin ya haɗa da Gwamnan Jihar Yobe, Mai Bala Buni a matsayin shugaba, yayin da Muiz Banire, tsohon Lauyan Jam’iyyar APC, ke a matsayin sakatare.
- Yadda Ake Inganta Tsarin Harkokin Kudi Na Dattawa A Kasar Sin
- Xi Jinping Ya Yi Muhimmin Bayani A Kan Ayyukan Kamfanoni Mallakar Gwamnati
Kwamitin ya haɗa da wasu gwamnoni, ministoci, da sauran mambobin jam’iyya.
Gwamna Buni ya ce kwamitin zai yi aiki da ƙwarewa wajen tsara dabaru da za su haɗa duk mambobin jam’iyyar, musamman waɗanda ke da ƙorafi, tare da magance rikice-rikice.
Ya kuma gargaɗi mambobin da su fifita muradin jam’iyya fiye da na ƙashin kansu.
Shugaba Tinubu ya jaddada buƙatar haɗin kai da juriya a jam’iyyar APC, inda ya tunatar da shugabannin jam’iyyar cewa an gina APC ne kan shiga tsakanin jama’a, bambancin ra’ayi, da siyasar ci gaba.
Ya ce kiyaye haɗin kai shi ne mabuɗin samun jam’iyya mai ƙarfi da ɗorewa.
Kwamitin zai kuma tsara dabaru don tabbatar da cewa APC ta shirya tunkarar zaɓen 2027, tare da ƙarfafa sadarwa da haɗin kai tsakanin mambobinta.