Sarki Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Bayan Shafe kwana 25 A Hannun Masu Garkuwa A Kwara
[ad_1]
Farin ciki ya lulluɓe al’ummar Bayagan-Ile da ke ƙaramar hukumar Ifelodun yayin da sarkinsu, Alhaji Kamilu Salami, Ojibara na Bayagan, ya shaƙi iskar ‘yanci daga hannun masu garkuwa da mutane.
Sarkin, wanda aka sace a ranar 29 ga Nuwamba, 2025, yayin da yaje kewayen gonarsa, ya koma gida da yammacin ranar Talata 23 ga watan Disamba.
- Dangote Kaɗai Ba Zai Iya Wadatar Da Nijeriya Man Fetur Ba, In Ji Manyan ‘Yan Kasuwa
- Xi Jinping Ya Yi Muhimmin Bayani A Kan Ayyukan Kamfanoni Mallakar Gwamnati
Majiyoyi na kusa da fadar sun tabbatar da cewa, sarkin a halin yanzu yana samun kulawar lafiya a wata cibiyar kula da lafiya da ba a bayyana ta ba, a cewarsu, yana “amsar magani” bayan ya shafe kusan wata guda a cikin daji.
Duk da cewa, dawowar Ojibara ta haifar da murna har da bukukuwa, amma hakan ya ƙara tsananta ƙiyayyar al’ummar ga Gwamnatin Jihar Kwara.
Tsawon makonni uku, iyalan masarautar Bayagan-Ile da shugabannin yankin sun yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su taimaka, amma a zarginsu, “an yi watsi da kokensu.”
An samu cewa, ƙoƙarin al’ummar yankin ne ya sanya aka kuɓutar da sarkin.
Har zuwa safiyar yau Laraba, rundunar ‘yansandan jihar Kwara da gwamnatin jihar ba su fitar da wata sanarwa a hukumance game da sakin sarkin ba.
[ad_2]
Source link