Super Falconets ta lashe gasar WAFU ta ’yan ƙasa da shekaru 20
[ad_1]
Tawagar matan Najeriya ’yan ƙasa da shekaru 20, Super Falconets, ta lashe gasar Yammacin Afirka ta bana WAFU B U-20, bayan ta doke Black Princesses ta Ghana da ci 3-0 a wasan ƙarshe da aka buga a safiyar Talata.
An fafata wasan ne a filin Stade Omnisports da ke Jamhuriyar Benin, inda Akekoromowei, Alaba Olabiyi da Ramotalahi Kareem suka zura ƙwallaye uku da suka bai wa Najeriya nasara.
Wannan shi ne karo na farko a tarihi da Super Falconets ke lashe wannan kofin tun lokacin da aka fara gasar.
Ghana, wadda ta lashe kofin a shekarar 2023, ta kammala wannan karo da maki shida kacal, yayin da Najeriya ta ɗaga kofin bayan samun nasara a duk wasanninta.
Yanzu hankalin Super Falconets zai koma kan wasan neman gurbin shiga gasar Kofin Duniya ta Mata ’Yan Ƙasa da Shekaru 20 ta 2026, inda za su kara da Senegal a watan Fabrairu mai zuwa.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link