Madalla Da Sabon Binciken Jami’ar Nankai Ta Kasar Sin Kan Mata Marasa Haihuwa



Hakika rashin haihuwa, wata babbar matsala ce da take dasa damuwa a zukatan ma’aurata da ba su samu rabon haihuwa ba. Musamman mata, sun fi shiga tsananin damuwa tun ma idan aka ce matsalar daga bangarensu take. Wannan matsala, ta kan zama alakakai ga duk iyaye da suka gamu da ita, tun daga mahudar rana har mafadarta, don haka ne ma ya sa masana kimiyya ke ci gaba da bincike don kara saukaka hanyoyin samun rabon haihuwa.

Jami’ar Nankai dake birnin Tianjing ita ma ta kawo dauki a wannan fanni, yayin da wata tawagar bincikenta ta gano wata sabuwar hanyar samun haihuwa ga matan da ake ganin juya ne (wadanda aka debe tsammanin haihuwarsu), inda hakan ya ba da sabon kwarin gwiwa ga matan da ke neman haihuwa, kamar yadda sakamakon binciken wanda aka wallafa a mujallar nazarin kwayoyin halitta ta “Cell Reports Medicine” ya nuna.

Dama dai an sani, yayin da mace ke kara yawan shekarun tsufa kwayayenta na haihuwa kan yi rauni sosai musamman ma daga shekaru 35, amma takamaime mene ne musabbabin hakan? Tawagar binciken jami’ar a karkashin jagorancin Farfesa Liu Lin, ta gano cewa, daga shekaru 34, kwayayen mata kan fuskanci sauye-sauye saboda yawaitar motsin tsarin tantanin halitta wanda ke da alhakin hada sinadaran ginuwar halitta. To, wannan ne yake wargaza tsarin aikin kwayayen ta yadda ko da mace ta saki kwai ba zai yi wani tasiri ba wurin daukar ciki.

Masu hikima kan ce, idan an gano matsala to an samu rabin maganinta, don haka bisa abubuwan da binciken ya gano, tawagar kwararrun jami’ar ta Nankai sun yi gwajin amfani da wani magani mai suna “rapamycin”, wanda ya yi shuhura wajen daidaita girman kwayoyin halitta, a cikin wasu samfuran beraye. Sakamakon gwajin ya nuna cewa, wannan maganin ya dawo da daidaiton tsarin aikin hada sinadaran ginuwar halitta yadda ya kamata, da kuma inganta kwayayen halitta da mata ke sakawa.

Da yake tsokaci kan wannan ci gaba da aka samu, wani likita daga Asibitin Yara na Shanxi dake kasar Sin Wu Xueqing ya ce, “Wannan binciken yana da matukar karfafa gwiwa a gare mu da marasa lafiya, bisa yadda ya bude wata sabuwar hanya ta fahimtar matsalar rashin haihuwa da kuma magance kalubalen rashin haihuwar musamman ta bangaren dake da alaka da tsufa.”

Ya kuma yi nuni da cewa, a binciken da za a yi na gaba, akwai bukatar gudanar da manyan gwaje-gwaje da za su mayar da hankali ga fadada nemo samfuran da za a yi aiki a kansu. Yana mai cewa, “har yanzu muna bukatar kara tabbatar da tasirin maganin da aka yi amfani da shi da kuma samar da nagartattun hanyoyin warkarwa ta yadda jami’an lafiya za su nakalci sahihin zabin da za su yi amfani da shi wajen magance matsalolin rashin haihuwa mabambanta, da kuma tabbatar da cimma muradun samun haihuwar.”

Tabbas, kamar yadda kasar Sin take da sa kwazo cikin abubuwan da take yi, ina da yakinin za a zurfafa wannan bincike domin cike gibin da aka gano don taimaka wa share hawayen iyaye masu neman haihuwa ruwa a jallo. (Abdulrazaq Yahuza Jere)



Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *