Gwamna Abba Ya Haɗa Zama Na Musamman Da Tsofaffin Ƴan Majalisar Kano
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi zama na musamman da tsofaffin ‘yan majalisar tarayya. Taron ya gudana a masaukin baki na gwamnatin Kano da ke Abuja.
Zaman ya haɗa manyan jiga-jigan ƴan siyasa daga jihar Kano a wuri guda. An tattauna batutuwan da suka shafi ci gaban jihar da ƙarfafa haɗin kai.
- Lokacin Cire Jar Hula Bai Yi Ba – Gwamnan Kano
- Matar Da Ta Haifi Ƴan Biyar A Kano Ta Rasu Bayan Haihuwa
Daga cikin mahalarta taron akwai Aminu Sulaiman Goro da Muhd Ali Wudil da Shaaban Sharada. Haka kuma sun haɗa da Abdullahi Mahmud Gaya da Hafizu Kawu da wasu tsofaffin ‘yan majalisa.
Gwamna Yusuf ya jaddada muhimmancin amfani da gogewar shugabannin da suka gabata. Ya ce hakan zai taimaka wajen ciyar da manufofin gwamnati gaba da tabbatar da ɗorewar ci gaba.

Mahallarta taron sun yaba da matakin da gwamnan ya ɗauka na haɗa kan ‘yan jihar. Sun bayyana taron a matsayin wata hanya ta ƙarfafa haɗin kai da ci gaba a Kano.