Musulman Kudancin Kaduna sun zargi manyan yankin da juya gaskiya

[ad_1]



Ƙungiyar Al’ummar Musulmi ta Kudancin Kaduna mai suna ‘Concerned Muslim Ummah’ ta zargi wasu manyan mutane a yankin da haifar da rarrabuwar kawuna da kuma juya tarihi domin cimma manufofin siyasa.

A taron manema labarai da ta gudanar a Kaduna, ƙungiyar ta yi watsi da iƙirarin cewa Kudancin Kaduna na da Kiristoci ne kaɗai.

Ta jaddada cewa Musulunci ya daɗe da wanzuwa a yankin tun ƙarnoni da suka gabata, inda ta ce Musulmi sun kai kusan kashi 40 cikin ɗari na al’ummar yankin.

Ƙungiyar ta ce tashe-tashen hankula kamar na Zangon Kataf a 1992 da rikicin bayan zaben 2011 sun tabbatar da cewa rikice-rikicen yankin ba wai na yanzu ba ne.

Ta kuma zargi wasu daga cikin manyan yankin da cin gajiyar rikice-rikice, nuna wariya ga Musulmi a masarautu, ƙirƙirar adadin jama’a saɓanin gaskiya da kuma yi wa gwamnati barazana.

Ta kuma jaddada rawar da Musulmi suka taka a zaɓuɓɓukan baya, ciki har da goyon bayan da suka bai wa Gwamna Uba Sani da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2023.

Yayin da ta yaba da salon mulkin haɗin kan gwamnan, ƙungiyar ta buƙace shi da ya ci gaba da yin taka-tsantsan daga siyasar barazana.

Haka kuma ta kira kafafen yada labarai da su riƙa bayar da rahoto bisa gaskiya tare da jan hankalin al’umma su guji siyasar rarrabuwar kawuna.

A ƙarshe, ƙungiyar ta sake jaddada goyon bayanta ga zaman lafiya da haɗin kai a Jihar Kaduna.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *