‘Yansanda Sun Ceto Mutum Ɗaya, Sun Kama Mace Da Zargin Garkuwa Da Mutane A Dajin Kwara

[ad_1]


Jami’an ‘Yansandan Jihar Kwara sun ceto wani wanda aka yi garkuwa da shi, mai suna Haruna Ahmadu, daga maɓoyar masu garkuwa da mutane a wani daji da ke Omu-Aran, hedikwatar karamar hukumar Irepodun ta Jihar.

‘Yansandan sun kuma kama wasu mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, Ayisa Ibrahim da Yakubu Hassan a yankin.

Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, Toun Ejire-Adeyemi, wanda ya sanar da wannan nasarar a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, ya ce ana ci gaba da kokarin kama sauran da suka tsere a yayin samamen a maɓoyarsu.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *