Arteta na neman wanda zai maye gurbin Merino
[ad_1]
Kocin Arsenal, Mikel Arteta, ya ce kulob ɗin na neman sabon ɗan wasa da zai maye gurbin Mikel Merino, wanda raunin da ya samu a ƙafarsa ta dama zai hana shi buga ragowar wasanni a wannan kakar.
Arteta ya ce rashin ɗan wasan tsakiyar a daidai wannan lokaci babban giɓi ne yayin da Arsenal ke hanƙoron lashe kofuna huɗu a wannan kaka.
Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa Arteta yana fatan ƙungiyar za ta samu madadin ɗan wasan gabanin rufe kasuwar musaya da cinikayyar ’yan ƙwallo a yammacin wannan Litinin ɗin.
Arteta ya ce dawowar Bukayo Saka da Kai Havertz da suka yi fama da jinya za ta ƙara wa ƙungiyar karsashi.
Arsenal na fatan kai bantenta gobe Talata bayan ta yi galaba kan Chelsea da ci 3-2 a zagaye na farko a wasan kusa da na ƙarshe na League Cup.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link